Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i| Hoto Daga: BBC
Gwamnatin jihar Kaduna ta sake yin gwajin kwarewa ga malaman firamare 35,000 a yunkurin ta na inganta ilimi a jihar.
Hakan na zuwa ne kusan shekaru hudu da gwamnatin tayi irin wannan jarabawar wanda ta kori malamai 22,000 sannan ta dauki kwararru 25,000.
A cewar shugaban hukumar kula da ilimi na SUBEB, Tijjani Abdullahi, jarabawar ba wai don a kori malami ba ne, sai dai a gano gibin da ake da shi a fannin darussa da nufin horar da malamai.
Tijjani ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da jarabawar da aka gudanar ta na'ura mai kwakwalwa a cibiyoyi uku a jihar.
Ya kara da cewa malaman "za su ga banbanci a tsarin jarabawar na bana."
Zaku tuna cewa Gwamnatin ta sallami malamai sama da 20,000 a shekarar 2017 sakamokon faduwar jarabawar cancantan da suka yi.
Hakan ya jawo cecekuce a tsakanin jama'a wanda har kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta nuna adawa ga gwamnatin jihar.
Daga bisani Gwamnatin ta dauki kwararrun malamai 25,000 don rufe gibin da aka samu.
0 Tsokaci