OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Dokar Ba-Aiki-Ba-Biyan Kuɗi shine Sharadin da ke kara jawoJinkiri Tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU – Adamu Adamu

Dokar Ba-Aiki-Ba-Biyan Kuɗi shine Sharadin da ke kara jawoJ

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya ce aiwatar da manufar gwamnatin tarayya ta ‘ba-aiki-ba-albashi’ shi ne kawai sharadin da ke kawo jinkirin sasantawa da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

 Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis din nan yayin da yake gabatar da jawabi a taron majalisar dokokin jihar karo na 47 a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ministan ya ce ASUU ba ta janye yajin aikin da take yi ba saboda bukatar a biya su dukkan albashin su da aka rike ya yin yajin aikin, wanda Ministan ya ce gwamnatin ba ta amince da haka ba.

Ya ce an samu daidaito kan sauran baƙatun  kungiyar.

Ministan, ya ce kungoyoyi huɗu daga cikin biyar na makarantun kasar sun amince za su janye yajin aikin nan da mako guda, inda za su sanar da haka bayan ganawa da sauran ƴan kungiyar ta su.

Dangane da batun biyan diyya ga daliban da aka batawa lokaci sakamakon yajin aikin da ya dauki watanni shida ana yi, ya ce wannan alhakin ASUU ne ba gwamnatin tarayya ba.

Ministan ya ce daliban da abin ya shafa su kai ASUU kotu domin a biya su diyyar lokacin da aka bata Musu.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ba ita ke da alhakin biyan miliyoyin daliban da aka tsaida musu karatu na tsawon watanni shida.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci