OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Dan Majalisa Mai Wakiltar Jihar Anambra A Zauren Majalisar Dokoki Ya Mutu A Kasar Afrika Ta Kudu

 Dan Majalisa Mai Wakiltar Jihar Anambra A Zauren Majalisar

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban masu rinjayi a zauren majalisar dokoki ta jihar Anambra, Okafor Nnamdi ya mutu a kasar Afrika ta Kudu dare Talatar da ta gabata.

Jaridar The Nation da ta wallafa labarin rasuwar ta bayyana cewa, Okafor Nnamdi ya ci zabe ne karkashin inuwar jam'iyyar All Progressive Grand Alliance, APGA a shekarar 2015. 

In da kafin Allah yayi masa cikawa yake a zango na biyu a matsayin dan majalisa kuma shugaban masu rinjaye.

Jaridar ta kara da cewa, bayanai basu bayyana dalilin mutuwar dan majalisar ba, har zuwa lokaci da ta wallafa wannan labari. 

Sai dai tace tana dakon karin bayani daga gurin majiyar ta dake da tare makusanatan mamacin.

 

Channels TV

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci