OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ci Gaba Da Mulkin Arewa Zai Haifar Da Tashin Hankali – Cewar Sarkin Iwo

Ci Gaba Da Mulkin Arewa Zai Haifar Da Tashin Hankali – Cew

Oluwo na Iwo a jihar Osun, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya yi gargadi kan ci gaba da rike madafun iko a Arewa a shekarar 2023, yana mai cewa idan hakan ta faru, hakan na iya kawo barazana.

Oba Akanbi, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaransa, Alli Ibraheem, wanda aka samu a Osogbo ranar Juma’a.

Ya ce barin mulki a Arewa zai rura wutar masu rajin bangarewa a ƙasar ta Yarbawa, wanda hakan zai basu hujjan ci gaba da hakan.

Yace masarautu da yankin nasu suna ƙoƙarin ganin zaman lafiya ta ɗore a yankin, Cewar Jaridar Punch.

A cewarsa, kokarin da sarakunan gargajiya a kudancin kasar suka yi ya kawar da tashin hankalin da ‘yan ta’addar kabilar Yarbawa suka haifar.

Sa'annan yayi kira ga sarakunan arewacin kasar da fitattun ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani domin tabbatar da mulki ya koma kudancin Najeriya a shekarar 2023.

Sanarwar ta kara da cewa, “Ni ina daga cikin  masu mulki daga Kudancin Najeriya da ke kawar da tashe-tashen hankulan al’ummar Yarabawa.  

"Nayi hakan ne don tabbatar da dunkulewar Najeriya, Bayan haka, masu tayar da hankali sun gabatar da batutuwa masu yawa don yin la'akari. 

"Muna fatan za'a lura da buƙatunsu don yin la'akari, Ba ma yin addu'a don sake ganin irin wannan zanga-zangar.  

"Za a iya dakile ta da adalcin siyasa gabanin babban zaben 2023, Kada siyasa ta wargaza kasar.

“Ina kira ga sarakunan gargajiya na Arewa da masu ruwa da tsaki da su yi la’akari da shugabancin Kudancin kasar domin a samu daidaito, daidaito da kuma hadin kai.  

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Arewa ya kusan cika wa’adi biyu na shekaru takwas, A gaskiya ya kamata mulki ya koma Kudu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci