OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Buhari Zai Sa Hannu Kan Kudirin Zabe A Wannan Makon, Cewar Dan Majalisa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai rattaba hannu a kan dokar gyaran zabe a wannan mako, a cewar wani dan majalisa.

 

Dan majalisa a majalisar wakilai, Hon. Serguis Ogun ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar ta yi gyare-gyaren da ya dace dangane da matsalolin da shugaban ya bayyana.

 

Ya kara da cewa hakan na nufin shugaban kasar ba shi da dalilin sake yin watsi da kudirin.

 

Jaridar AllNews ta ruwaito cewa shugaban ya ki amincewa da kudurin dokar ne biyo bayan kura-kuran da aka samu a cikin batutuwan da suka shafi tsarin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa.

 

Sai dai Majalisar ta yi aiki da shawarwarin kuma ta mika wa shugaban kasa don amincewar sa.

 

A wata hira da jaridar Vanguard, dan majalisar ya bayyana cewa, "Na tabbata zai sanya hannu kan kudirin dokar a cikin makon nan."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci