OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Asibitin Abdullahi Wase Ya Kera Na'urar Rarraba Iskar Oxygen

Asibitin Abdullahi Wase Ya Kera Na'urar Rarraba Iskar Oxygen

The oxygen splitter home made in it's entirety

Likitoci a asibitin Abdullahi Wase, wato asibitin Nassarawa sun samu nasarar kera na’urar da zata taimaka wajen rarraba iskar oxygen ga marasa lafiya hudu a lokaci guda.

Wata sanarwa da hukumar kula da manyan asibitoci ta jiha ta fitar mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran ta, Ibrahim Abdullahi ta ce an samu nasarar kera nau’urar ne bayan samun horo shekaru hudu da suka gabata daga wajen wani likita a dan asalin kasar Germany.

Da yake Karin haske kan batun, shugaban sashen gyare-gyare na asibitin, Injiniya AbdulKadir Abdu Abba yace hadin kai tsakanin dukkan ma’aikatan asibitin ya taka muhimmiyar rawa wajen kera na’urar.

Ya ce na’urar zata taimaka wajen rage kudin da asibitin ke kashewa wajen siyo iskar oxygen din.

Injiniya Abba wanda yace duk kayan aikin kera na’urar a nan aka same su, ya yabawa shugabancin asibitin bisa goyon baya da suka basu wajen samun wannan nasara,

Da yake yi mana bayani, Shugaban Asibitin, Dakta Mustapha Hikima ya ce la’akari da yadda asibitin ya yi ta siyan iskar gas, musamman a lokacin bullar cutar korona, yasa injiniyoyi da likitocin suka yi tunanin samar da tasu na’urar.

Ya ce zasu nunawa sauran asibitocin dake karkashin kulawar hukumar dake kula da manyan asibitocin Kano yadda zasu samar da irin wannan na’ura domin inganta lafiyar al’umar jihar.

Dakta Hikima ya yabawa injiniyoyin da dukkan wadanda suka taimaka wajen kera na’urar, inda ya bayar da tabbacin ci gaba da karfafawa likitocin dake asibitin gwiwa domin inganta lafiyar al’ummar Kano.

Ya kuma godewa gwamna Ganduje bisa goyon baya da yake bawa sashen bangaren lafiya a jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci