OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Kano Za Ta Yi Aikin Hadin Gwiwa Da Gwamnatin Tarayya Wajen Magance Tarin Fuka

Gwamnatin Kano Za Ta Yi Aikin Hadin Gwiwa Da Gwamnatin Taray

Taswirar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta yi aikin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya domin yaki da cutar tarin Fuka, yayin da ta ƙaddamar da babies masu kafa uku na gwajin tafi-da-gidan ka.

Yayin da yake kaddamar da babura masu kafa uku a Kano, Kwamishinan lafiya na jiha, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa yace jami'an lafiya zasu dinga zuwa har gidajen jama'a domin gwajin cutar Tarin-fuka karkashin shirin da gwamnatin tarayya ta samar a Kano.

Ya ce wannan shiri ya zo dai dai da kudurin gwamnatin jihar Kano, kuma zai taimaka wajen rage yaɗuwar cutar tsakanin mazauna jihar.

Aminu Tsanyawa ya ba da tabbacin ganin an yi amfani da su ta hanyar da ta dace, tare da bukatar samun karin na’urori na musamman domin samar wa a dukkanin manyan masarautun jihar guda biyar.

Da yake Karin haske, Dakta Ibrahim Aliyu Umar shugaban sashin yaki da cutar Tarin-fuka a ma’aikatar lafiya ta jiha ya ce an samar da na’urori ta hanyar Babura masu kafa Uku domin shiga lungu da sako domin gwajin cutar da Kuma fara dora mara lafiya kan magani idan an tabbatar yana dauke da cutar.

Ibrahim Umar ya ce na’urorin na gwajin cutar ta hanyar amfani da Babura masu kafa Uku gwamnatin tarayya ta samar da guda biyar ne a duk fadin kasar nan Wanda Kuma aka bai wa jihar Kano guda biyu ne bisa la’akari da yadda ta ke tallafawa sha’anin lafiya a jihar.

Ya Kara da cewa baya ga gwajin cutar Tarin-fuka, na’urorin suna yin gwajin cututtukan suga da hawan jini nan take.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai