OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

An Kuma, 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Biyu, Sun Yi Garkuwa Da 20 A Kaduna

An Kuma, 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Biyu, Sun Yi Garkuwa D

Hoto Daga: PremiumTimes

'Yan bindiga sun kai hari kauyen Unguwan Gimbiya dake karamar hukumar Chikun dake Kaduna.

'Yan bindigan su kashe mutum biyu tare da sace sama da mutane 20.

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, lamarin ya faru ne da karfe daya na safiyar jumma'a.

Jalige ya bayyana cewa 'yan bindigan sun yi ta harbi a iska kafin su kashe mutanen biyu tare da tafiya da wasu sama da ashirin.

Sun sace mutanen ne kafin isowar jami'an tsaro don kawo musu dauki.

Jalige ya kara da cewa hadin gwiwa ta jami’an tsaro suna kokarin ceto wadanda aka sacen tare da kamo masu laifin.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci