OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Wata Kungiyar Arewa Ta Nuna Goyon Bayan Tinubu

2023: Wata Kungiyar Arewa Ta Nuna Goyon Bayan Tinubu

Kungiyar Arewa Solidarity Group (ASG) ta nuna goyon bayan ta ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu gabanin zaben 2023.

Kungiyar ta ce tsarin tattalin arzikin dan takarar shugaban kasan ne abin da kasar ke bukata a halin yanzu.

Shugaban kungiyar Isa Ahmed ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai a ranar Alhamis a Kaduna.

A cewar Ahmed: “Kamar yadda Tinubu ya ce, manyan kalubalen tattalin arzikin mu su ne rashin zuba jari da gudanar da aiki mai inganci, kuma wadannan su ne abin da ya kamata ya duba, idan ya zama shugaban kasa a 2023.”

Ya kara da cewa gina tattalin arziki zai inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Ya kuma kara da cewa manufar Tinubu ba za ta iya tabbata ba sai ta hanyar kishin kasa, adalci da kuma nuna ‘yan uwantaka.

Ahmed ya kuma bayyana cewa kungiyar za ta goyi bayan Tinubu ne saboda jajircewar sa na tallafa wa ‘yan kasuwa masu zaman kan su tare da jawo hankalin masu zuba jari kai tsaye daga kasashen waje domin magance matsalar rashin aikin yi a kasar.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su biye kungiyar domin mara wa burin takarar Tinubu na shugaban kasa a jam’iyyar APC. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci