OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Zan Yi Nazari Kan Bukatar Sakin Nnamdi Kanu- Shugaban Kasa

Zan Yi Nazari Kan Bukatar Sakin Nnamdi Kanu- Shugaban Kasa

PRESIDENT-BUHARIS-AUDIENCE-WITHHIGHLY-RESPECTED-IGBO-GREATS

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin yin nazari kan bukatar ƙungiyar dattawan al'ummar Ibo na a saki shugaban kungiyar ‘yan a ware ta IPOB, Nnamdi Kanu.

Shugaba Buhari ya ayyana hakan ne a ranar Juma’a lokacin da ya karbi bakuncin dattawan karkashin jagorancin tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama Mbazulike Amaechi da ministan Kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige a birnin tarayya Abuja.

Ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai bawa shugaban kasa shawara kan kafofin yada labarai, Femi Adeshina, Buhari ya ce lamarin mai wuya ne, musamman ma tunda yana gaban kotu.

Ya jaddada cewa tunda lamarin na gaban kotu, idan har ya shiga tsakani zai sabawa tanadin tsarin mulkin kasa da ya shata iyaka tsakanin gwamnati da bangaren shari’a.

”Kun zo da bukata mai matukar wahala gare ni a matsayi na na shugaban wannan kasa”. Tasirin bukatar kuma na da girman gaske.

“A shekaru shida da nake shugaban kasa, ba wanda zai ce na yi katsalandan cikin ayyukan sashin shari’a”

”Ubangiji ya baku tsayin kwana, ya kuma baku lafiyayyen tunani a wadannan shekaru naku. Da yawa daga mutane masu rabin shekarun ku sun shiga rudu. Amma bukatar da kuka zo da ita na da nauyi. Zan yi nazari a kai.

Shugaba Buhari ya ce yana ganin a bawa Kanu dama ya wanke kan sa a gaban kotu ma alfarma ce aka yi masa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci