OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zan Fitar Da Najeriya Daga Cikin Duhu —Atiku Abubakar

Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin fitar da Najeriya daga cikin rashin hasken wutar lantarki.

Atiku na wannan batu ne biyo bayan yajin aikin da ma’aikatan wutar lantarkin suka shiga a Larabar da ta gabata, wanda ya kai ga rufe manyan tashoshin wutar lantarki.

In zaku iya tunawa,  wutar lantarkin ta dawo ne bayan da ma’aikatan suka amince da dakatar da yajin aikin na tsawon makonni biyu.

Da yake mayar da martani ta shafin Twitter,  tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi alkawarin mayar da hankali wajen magance matsalar wutar lantarki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Atiku ya yi ikirarin cewa manufarsa na da nufin jawo jarin da ya dace a bangaren wutar lantarki.

“Bayan na lura da abinda ke faruwa a fannin wutar lantarki a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, na sake gamsuwa da cewa mafita ta kan matsalar wutar lantarki, kamar yadda yake kunshe a cikin daftarin manufofina.

"Alkwarin da na yi da ‘yan Nijeriya, shi ne shirin da ya fi daukar hankali wajen fitar da Najeriya daga duhu," in ji shi.

Atiku Abubakar ya kuma ƙara da cewa, ɗaya daga hanyoyin cimma wannan manufa ita ce mika ragamar samar da hasken wutar lantarki ga gwamnatocin jihohin kasar nan, tare da neman ƴan kasuwa su zuba hannun jari a ɓangaren.

 Ya ce bai kamata wani sabani da gwamnatin tarayya ya shafi ɗan Najeriya dake sauran jihohin kasar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci