OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Zaben Shugaban Kasa a 2023: ‘A shirye nake na kutsa kai’ – Tinubu

APC Chieftain and Presidential Aspirant of the APC, Bola Ahmed Tinubu|

Wani jigo kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu ya jaddada muradin sa na zama shugaban kasa a zaben 2023.

 

Tinubu ya bayyana hakan ne a wata ziyarar tuntuba da ya kai wa sarkin(Alafin) OYo, Oba Lamidi Adeyemi da Oba Lekan Balogun a ranar Lahadi.

 

Tinubu ya bayyana cewa, "Babu wata barazana da za ta iya hana ni, a shirye nake in kutsa, zan zama shugaban Najeriya, muna cikin tsaka mai wuya."

 

Dan takarar shugaban kasan kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Tinubu, ya yi magana a fadar Alafin din inda ya bukaci goyon bayan dattawan gargajiya na yankin.

 

Ya bayyana cewa, “Ba zan iya fara aiki mai girma irin wannan ba, ba tare da neman addu’a da hadin kan sarakunan gargajiya ba.

 

“Na zo nan ne domin in sanar da iyayen mu shawarar da na yi na tsayawa takarar shugabancin kasar nan a 2023. Abin da nake bukata daga sarakunan mu da aka fi sani da su shi ne addu’a da hadin kai.

 

“A yau, da yardar Allah ta musamman a kasar Yarbawa sabanin a baya muna da Mataimakin Shugaban kasa, Ministan Ayyuka, Cikin Gida da Wasanni amma har yanzu muna bukatar kari,” inji Tinubu kamar yadda Jaridar Vanguard ta ruwaito.

 

A nasa jawabin, Oba Adeyemi yayin da yake kira ga ruhin kakanninsa yace sun amince da takarar har da sarakunan Oke-Ogun guda 10 da suka halarta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci