OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

YANZU-YANZU: Makinde Ya Maye Gurbin Tambuwal A Matsayin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP

YANZU-YANZU: Makinde Ya Maye Gurbin Tambuwal A Matsayin Shug

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP.

Makinde ya zama sabon shugaban ‘yan mintoci kadan bayan tsohon shugaban, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya yi murabus daga mukamin a ranar Alhamis.

Gwamnan jihar Oyo ya zama sabon shugaban ne a taron majalisar zartarwa na jam’iyyar PDP da ke gudana a babban birnin tarayya Abuja.

An ruwaito cewa hukumar zabe ta kada kuri'ar amincewa da shugaban jam'iyyar PDP na kasa Sanata Iyorchia Ayu, wanda hakan ya sanya wasu jiga-jigan jam'iyyar suka koka kan ficewar sa, cewar Jaridar Punch.

Mambobin kwamitin 397 da suka hada da tsofaffin shugabannin jam’iyyar na kasa, tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da dai sauransu ne aka tantance su a taron.

Dukkan ‘yan kwamitin 397 da suka halarci taron sun kada kuri’ar goyon bayan Ayu ya ci gaba da zama shugaban jam’iyyar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci