OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Sandan INTERPOL Sun Kama Yan Najeriya Masu Damfara A Shafin Intanet

Yan Sandan INTERPOL Sun Kama Yan Najeriya Masu Damfara A Sha

 A wani samame da hukumar  INTERPOL ta jagoranta ta kai ga kama wasu mutane 75 da ake kyautata zaton suna da alaka da wata kungiyar damfarar intanet a Najeriya da ta sace miliyoyin kudade.

 Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da kwanan watan Juma'ar da ta gaba.

Sanarwar ta bayyana Yan Sandan INTERPOL sun lura da salon rayuwar da yawa daga cikin wadanda ake zargin da sa hannun su wajen damfarar.

Hakan ya sa suka gudanar da sumame har sau 49, Inda sukayi nasarar kwace layin waya wato SIM 12,000 a lokacin aiwatar da sumamen mai suna ‘Operation Jackal’ wanda ya gudana daga ranar 26 ga Satumba zuwa 30 ga Satumba.

Hakazalika jami'an sun kama wasu kadarori  da suka hada da gidaje da motoci na alfarma uku da kuma dubunnan kudade.

 ‘Yan sandan  sun maida hankali kan bata garin Najeriya da Afrika ta Kudu. Baya ga mutane 75 da aka kama, ‘yan sanda sun kwato kudi Yuro miliyan 1.2 a wasu asusun banki da dama.

 Stephen Kavanagh, babban daraktan ayyukan ‘yan sanda na INTERPOL ya bayyana cewar "mun shaida yadda ƙungiyoyin aikata laifuka irin su Black Ax su kamyi amfani da kuɗin da aka samu daga zamba ta yanar gizo zuwa wasu wuraren aikata laifuka, kamar su miyagun ƙwayoyi da fataucin mutane,” 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci