OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Sanda Sun Kama Mutum 3 Bisa Laifin Kashe Wata Mata A Ibadan

'Yan Sanda Sun Kama Mutum 3 Bisa Laifin Kashe Wata Mata A Ib

Rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo ta cafke wasu mutane hudu da ake zargi da kashe wata budurwa ‘yar shekara 18 mai suna Eniola a makon jiya a Ibadan.

 

 Wadanda ake zargin da aka kama kuma aka tsare tun ranar Juma’a suna fuskantar tambayoyi a sashin binciken manyan laifuka na Iyaganku a jihar Ibadan.

 

Jaridar daily trust ta ruwaito cewa an kashe matar a wani otal da ke kusa da titin Iwo a Ibadan, babban birnin jihar a makon jiya.

 

 Rahotanni sun ce marigayiyar ta bi wasu kawayenta da ba a kai ga gano ko su waye ba zuwa bikin Birthday a wani otal a lokacin da wannan mummunan lamari ya faru.

 

 Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Adewale Osifeso, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike game da alamarin.

 

Ya kuma tabbatar da cewar za a cigaba da bayar da bayanai ga manema labarai a lokacin daya dace. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci