OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan sanda sun kama masu ba da bayanan sirri ga yan bindiga a jihar Katsina

'Yan sanda sun kama masu ba da bayanan sirri ga yan bindiga

Nigerian Police force

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu mutane uku Yan leken asirin wata kungiyar masu garkuwa da sukayi garkuwa da mata da ‘ya’yan wani dan majalisar wakilai, Hon. Dr Ibrahim Aminu, a jihar Katsina.

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Lahadi.

Olumuyiwa Adejobi ya kara da cewa bayan rahoton sirri kan ayyukan ‘yan ta’addan da jami’an IRT da ke aiki da Operation Restore Hope na rundunar suka samu a kauyen Yankwani da kuma garin Kurani, rundunar ta kai dauki tare da cafke wadanda ake zargi da yin garkuwa da iyalan dan majalisar hadi da wasu mutanen da akayi garkuwa dasu a maboyar su daban-daban.

Ya kara da cewa, manyan mutane ukun da ake zargi sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa yayin gudanar da bincike.

Jami’an IRT sun kama wadanda ake zargi  Muttaka Ibrahim, Suleiman Rabiu, da Surajo dukkansu ‘yan asalin karamar hukumar Bakori ne bisa zargin su da bayar da bayanan da suka kai ga harin da aka kai wa dan majalisar inda aka yi garkuwa da iyalin shi.

A yayin bincike, Muttaka Ibrahim ya amsa laifin da ake zargin sa da cewa shi da sauran wadanda aka kama ‘yan kungiyar asiri ne ga wani kasurgumin dan ta'adda mai suna Sani Tukur wanda aka fi sani da Abacha wanda ya addabi mutanen kauyuka da garuruwan  jihohin Katsina da Zamfara.

Sauran wadanda har yanzu suke hannun 'yan ta'addan sun hada da Buhari Usman wanda aka fi sani da Fedeco, Nazaradeen Ibrahim, Amandallah Ahmad, Ibrahim Suleiman, Sumayya Nura, da Yahaya Bura.

Masu garkuwa da mutanen, bayan sun yi garkuwa da matar dan majalisar, Rabi Yusuf da ’ya’yansa maza biyu sun bukaci a basu naira miliyan goma sha daya kuma an badu kana suka bukaci naira miliyan goma.

A cewar ‘yan sandan, daya daga cikin ‘yan fashin mai suna Muttaka Ibrahim, ya amsa cewa an biya su Naira 130,000.

Ya kuma yarda cewa shugaban masu garkuwar ya karbi jimillar naira miliyan shida da dubu dari biyar daga wadanda suka yi garkuwa da su a garin Yankwani.

Da yake bayyana irin halin da ya shiga, dan majalisar ya shaida wa ‘yan sanda masu binciken cewa ya biya jimillar kudi har miliyan talatin da bakwai da naira dubu dari biyar ga shugaban kungiyar domin a sako iyalan shi.

Kakakin rundunar Yan Sandan Mista Adejobi ya bayyana cewa, suna cigaba da gudanar da bincike akan wadanda ake zargin kuma za a gurfanar da su a gaban kotu idan aka same su da aikata laifin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci