OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Bindiga sun yi garkuwa da mutane 45 a wani Coci a jihar Kaduna

Yan Bindiga sun yi garkuwa da mutane 45 a wani Coci a jihar

Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari cocin Cherubim Seraphim a unguwar Bayan Kasuwa da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Yan bindigan sunkai hari ne a yayin da masu ibadar ke tsaka da bauta,inda suka yi awon gaba da kimanin mutane 45.

Kungiyar ‘yan sandan Kudancin Kaduna (SOKAPU) ita ta shaida wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Litinin.

Shugaban kungiyar ta SOKAPO, Awemi Maisamari, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da masu ibada sama da mutum 45 tare da wasu mazauna yankin.

Mista Maisamari ya ce masu garkuwar sun tuntubi wasu daga cikin iyalan wadanda suka sace.

Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a garin Kajuru da ke Kudancin Kaduna da ma sauran kananan hukumomin jihar shine babban abinda yafi zama ruwan dare.

Wadanda abin ya shafa sun hada da malamai, ’yan kasuwa, da sauran mazauna garin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci