OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

‘Yan Bindiga Sun Kara Kai Hari Kaduna, Sun Kashe Mutane 15

‘Yan Bindiga Sun Kara Kai Hari Kaduna, Sun Kashe Mutane 15

Photo Source: PremiumTimes

Bayan wani harin da ‘yan bindiga suka kai wani kauyen Kaduna, an kashe mutane 15.

‘Yan bindigan sun kai hari kauyen Hayin Kanwa da ke Yakawada a karamar hukumar Giwa a ranar Lahadi.

Hakan na faruwa ne kwanaki uku bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 50 a karamar hukumar.

Wani da ya nemi a sakaya sunan sa yace an yi jana’izar mutanen ne a ranar Litinin.

Ya Kuma koka da yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara ganin yadda ake samun mace-mace a kullum tun ranar Alhamis.

Wani dan banga kuma ya shaida wa Daily Trust cewa, “Al’amarin ya yi muni saboda wasu ‘yan bindiga sun kashe karin mutane 15 a Hayin Kanwa a daren jiya Lahadi.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun kai hari kan al’ummar garin suna harbe-harbe, inda ya ce gawarwakin mutanen da suka mutu a harin da aka kai a daren Lahadin sai da safe aka kwashe su.

Wata majiyar kuma ta yi zargin cewa ‘yan bindigan a yanzu sun fi sha’awar kashe mutane akan sace su.

Gwamnati ko ‘yan sanda ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci