OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kara Kashe Mutum 23, Da Sace Dayawa A Giwa

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kara Kashe Mutum 23, Da Sace Dayaw

Wasu ‘yan bindiga sun sake kashe wasu mutane 23 tare da raunata wasu da dama a wasu kauyuka biyu na karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Wannan dai shi ne hari na hudu a jere da ‘yan bindiga suka kai a cikin mako guda a kauyukan karamar hukumar.

Kauyukan da ‘yan bindigar suka kai hari sun hada da Anguwar Maiwa da Anguwar Kanwa. 

Wani ganau ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyukan ne da misalin karfe 1:00 na safiyar ranar Talata.

A cewar sa, tun karfe biyar na yemmacin ranar litin aka ga 'yan bindigan suna taruwa akan babura, wanda hakan yasa aka sanar da jami'an tsaro.

Ya kara da cewa ba'a kawo musu dauki ba har aka kai musu harin.

Daga bisani an samu taimakon jami'an tsaro bayan kashe mutane 23 da akayi, sai dai su ma jami'an tsaron sun yi rawar gani wurin kwato wasu tare da kashe 'yan bindigan da dama.

Rundunar 'yansandan Jihar Kaduna bata fitar da wata sanarwa ba.

Haka kuma yunkurin samun kakakin rundunar, ASP Mohammed Jalige yaci tura.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci