OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Wani Uba Da Ya Kashe Dan Sa Mai Shekara 7 Akan Kudi Ya Shiga Hannu

Wani Uba Da Ya Kashe Dan Sa Mai Shekara 7 Akan Kudi Ya Shiga

‘Yan sanda sun yi nasarar damke wani uba dan shekaru 36 a jihar Enugu bayan kashe dan sa da yayi kana ya binne shi.

Uban mai suna Chidi Onyishi ya kashe dan nasa ne dan shekaru 7 domin asirin samun kudi.

Wanda ake zargin ya hada baki da wani makahon Fasto ne mai shekaru 95, Okeke Eneokwor, don kashe dan nasa.

A ranar 22 ga watan Oktoba ne Chidi ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa dansa mai shekaru 7, Chimdalu Chidi, ya bace amma daga baya aka gano cewa shi da kansa ya kashe dan.

An gano cewa bayan kashe shi, ya binne gawar a wani rami mara zurfi kusa da wani kogi a Abakpa Nike kwanaki biyu kafin ya kai karar, wanda hakan ya faru ne karkashin Jagorancin Faston. 

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sanda a Enugu, Daniel Ndukwe ya fitar, an kama wanda ya aikata laifin tare da wanda ake zarginsa da shi, wadanda dukkansu suka jagoranci ‘yan sandan zuwa bakin kogi inda aka tono gawar yaron.

“Bincike na farko ya nuna cewa ya amsa laifin sa kuma ya jagoranci jami’an ‘yan sanda suka kama wani Fasto Okeke Eneokwor mai shekaru 95 da aka ce makaho ne da kuma mazaunin Dental Avenue, Trans-Ekulu, Enugu, wanda ya nuna a matsayin abokin aika-aikan.

 

“Ya kuma jagoranci jami’an ‘yan sanda da tawagar likitoci zuwa wani rafi a Abakpa-Nike, Enugu, inda aka tono gawar karamin yaron daga wani kabari mara zurfi bayan da shi da abokin aika-aikan suka kashe tare da binne yaron a ranar 20/10/2021.

 

“A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Abubakar Lawal, ya umurci hukumar CID ta jihar Enugu da ta gudanar da kwakkwaran bincike wanda zai kai ga gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a cikin lamarin.

 

“Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar da su kasance masu lura, masu bin doka da oda, tare da gaggauta kai rahoton masu aikata laifuka da ayyukansu ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma ta hanyar kiran layukan gaggawa na rundunar ta 08032003702, 08075390883 ko 08086671202."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci