OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojojin Najeriya Sun Kama Tabar Wiwi 792 a Ogun

Sojojin Najeriya Sun Kama Tabar Wiwi 792 a Ogun

Sojojin Najeriya na runduna ta 81, sun kama wasu haramtattun kwayoyi guda 792, wadanda ake zargin tabar wiwi ce nau'in cannabis sativa, a yankin Ilaro na jihar Ogun.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Manjo Olaniyi Osoba, mai magana da yawun kungiyar Divison, ya sanyawa hannu a ranar Juma’a.

 A cewar Osoba, kame magungunan ya biyo bayan wani samame da jami’an leken asiri suka yi a wani shingen bincike da ke kan iyakar Ilaro da Jamhuriyar Benin.

Manjo Osoba ya bayyana cewar an boye fakitin wiwi din a cikin wata babbar mota da ta fito daga yankin Volta na kasar Ghana.

Osoba ya ce binciken da aka yi kan motar da ke dauke da kayan ya bayyana an kera ta ne musamman domin safarar miyagun kwayoyi.

 “An kiyasta cewa miyagun kwayoyi da ake zargin sun kai kimanin naira miliyan goma, kuma za a kai su ga wata haramtacciyar cibiyar hada magunguna da ke Legas mallakin wasu bata gari.

 Sojojin da ke shingen bincike sun fara zargin cewar bata gari ne masu motar bayan da suka yi musu tayin cin hanci, Hakan yasa suka bincika suka kuma gano magungunan da aka boye bayan sun bijirewa cin hancin da ake zargin kungiyar safari miyagun kwayoyin ta bayar.” inji shi.

Osoba ya bayyana cewa, an mika miyagun kwayoyin ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) da ke Legas domin ci gaba da daukar mataki. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci