OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rundunar Ƴan Sandan Enugu Na Binciken Jami'in Ta Kan Zargin Yiwa Matashiya Fyade

Rundunar Ƴan Sandan Enugu Na Binciken Jami'in Ta Kan Zargin

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Enugu, Ahmed Ammani, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan wani mataimakin Sufetan ‘yan sanda (ASP) kan fyade da ake zargin ya yi wa wata matashiya.

Sufeton dai yana aiki ne a ofishin yan sanda da ke Agwu a jihar.

kakakin rundunar yan sandan jihar, Daniel Ndukwe shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Ammani ya umarci ma’aikatar leken asiri da binciken manyan laifuka ta jihar da ta gudanar da cikakken bincike tare da gabatar da “sakamako” kan zargin.

Ya ce wacce lamarin ya ritsa da ita ta kasance ‘yar kimanin shekara 17 wacce ta ke tsare a ofishin ‘yan sandan.

A cewarsa, duk da cewa lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Maris, amma sai a yanzu ne 'yan uwan yarinyar suka kai rahoto.

“Kwamishinan ya kuma ba da umarnin a kammala binciken cikin kankanin lokaci.

ya kuma bada tabbacin hukunta wannan Sifeta ta re da ma duk wani wanda ya aikata irin wannan laifin” in ji Mista Ndukwe, mataimakin sufetan ‘yan sanda.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci