OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Majalisar Wakilai Ta Nemi Aba Wa Gwarazan Aji Masu Digiri Aiki

Majalisar Wakilai Ta Nemi Aba Wa Gwarazan Aji  Masu Digiri A

Majalisar wakilai ta yi kira ga ma’aikatu da hukumomin tarayya da su yi la’akari da baiwa daliban gwarazan aji da suka kammala digiri aiki kai tsaye.

Majalisar ta yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin zaman ta.

Hon. Chinedu Emeka Martins ya lura cewa yayin da jami'o'in Najeriya ke samar da daruruwan masu digiri na farko a duk shekara, samun ayyukan yi ya yi wuya.

Ya bayyana cewa yayin da gwarazan ke zama marasa aikin yi, wadanda ke baya kuma suna samun damar a dauke su aiki saboda suna da masu tsaya musu.

Ya ce ya zama wajibi a dauki wadanda suka zama gwarazan aji aiki, ta yadda za a samu shugabannin da za su ciyar da kasa gaba.

Ya ci gaba da cewa bai wa wadanda suka kammala karatun digiri a matsayin gwaraza aikin yi zai sa wasu su ga cewa aiki tukuru yana da riba.

Majalisar ta kuma bukaci ma’aikatar ilimi da ta yi hulda da sauran ma'aikatu don tabbatar da an dauki wadanda suka kammala digiri a matsayin gwaraza.

Majalisar ta kuma umarci kwamitocinta masu kula da manyan makarantu da samar da ayyukan yi don tabbatar da bin doka da oda.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci