OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kwararriya A Fannin Abinci Ta Yi Gargaɗi Kan Siyan Abincin Da Aka Dafa Kusa Da Juji

Kwararriya A Fannin Abinci Ta Yi Gargaɗi Kan Siyan Abincin

Wata kwararriya a fannin abincin a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, AKTH, Rumanatu Abdulmalik ta gargadi ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan wajen siyan dafaffen abinci da ake siyarwa kusa da juji.

Rumanatu Abdulmalik ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ranar Lahadi a Abuja, cewa duk mai siyan irin wannan abinci zai iya kamuwa da gubar abinci ko kuma gurbacewar abinci daga kwayoyin cuta.

Ta ce rashin tsaftar abinci mai kyau zai iya haifar da gubar abinci daga kwayoyin halittar da ke cikin ruwa, iska da kuma hannaye, wanda ke haifar da illa ga lafiyar ɗan Adam.

"Yana iya haifar da kamuwa da cutar jini ta hanyar cin kwayoyin cuta, gudawa,zazzabin typhoid, cutar kwasharko da sauran cututtuka masu tsanani kamar ciwon koda, hepatitis da aka sani da ciwon hanta da sauran cututtuka," in ji ta.

Ƙwararriyar ta ce ba duk masu sayar da abinci ba ne suka san yadda ake sarrafa abinci don hana asarar sinadarai da ka iya haifar da rashin abinci mai gina jiki.

"Ma'aikatar lafiya da sauran masu ruwa da tsaki sun gudanar da wayar da kan masu siyar da abinci, masu saye da sauran jama'a kan cin abinci mai tsafta da lafiya," in ji ta. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci