OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Oborevwori A Matsayin Dan Takarar Gwamnan PDP A Jihar Delta

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Oborevwori A Matsayin Dan Takarar

PDP and court

Kotun koli, a yau Juma’a, ta tabbatar da kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Sherrif Oborevwori, a matsayin dan takarar jam’iyyar  PDP, a zaben gwamna mai zuwa a jihar Delta.

 Kotun kolin, a wani mataki na bai daya da kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin mai shari’a Amina Augie ta yi watsi da karar da wani dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar, Olorogun David Edevbie ya shigar kan Oborevwori.

 Edevbie ya daukaka kara, inda ya yi zargin cewa Oborevwori ya mikawa jam’iyyar PDP takardun karya da na jabu, domin neman cancantar tsayawa takara a zaben da aka gabatar a ranar 11 ga Maris, 2023.

 Ya shaida wa kotun cewa Oborevwori yana da a cikin takardar Karatun da ya gabatar, ya ce an haife shi ne a shekarar 1963, amma ya ba da takardar shaidar jarabawar WAEC wadda aka ba wani da aka haifa a shekarar 1979.

 Mai shigar da karar ya dage cewa duk takardun da Oborevwori ya mika wa jam’iyyarsa, na goyon bayan cancantarsa ​​na tsayawa takara, bai dace da sunansa ba a lokacin da aka haife shi.

 Bayan haka, Edevbie, ya ce shari'ar ta ba da dama ta musamman ga Kotun Koli tayi amfani da sashe na 29 (5) na sabuwar dokar zaben 2022.

 Ya ce sashin ya tanadi cewa duk wani mai neman tsayawa takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar siyasa kuma yana da hujjar cewa duk wani bayani da dan takarar jam’iyyarsa ya bayar dangane da sharuddan da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada na cancantar yin zabe karya ne, zai iya zuwa kotu don kalubalantar cancantar irin wannan dan takarar.

 Sai dai a hukuncin da ta yanke, kotun kolin ta ce zargin da wanda ya shigar da kara ya gabatar babban laifi ne don haka ya kamata a tabbatar da shi ba tare da wata shakka ba.

 An lura da cewa saboda "duban zarge-zarge na zamba, wakilci na karya da kuma na jabu na takardu" da aka yi wa Oborevwori, wanda ya shigar da kara, ya kamata ya fara aikinsa ta hanyar Rubutun Sammaci wanda zai ba da damar kotun da ta yanke hukunci ta bukaci shaidu domin fadada bincike.

 Kotun Koli ta tabbatar da cewa ba za a iya warware zarge zargen Edevbie akan Oborevwori ba ta hanyar shigar da takardun rantsuwa.

 Bugu da kari, kotun kolin, ta ce karar Edevbie tamkar Riga malam Masallaci ce domin PDP ba ta mika sunan Oborevwori ga hukumar zabe mai zaman kanta, INEC a matsayin dan takara ba a lokacin da ya shigar da karar.

A hukuncin da kotun kolin ta yanke, mai shari’a Tijjani Abubakar, ya ce bai ga dalilin yin watsi da hukuncin kotun daukaka kara da tun farko ta tabbatar da nadin Oborevwori ba don haka yayi watsi da ita.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci