OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumomin Amurka Na Neman Wani Dan Najeriya Akan Damfarar Miliyan 30

Hukumomin Amurka Na Neman Wani Dan Najeriya Akan Damfarar Mi

Hukumomin Amurka na neman Chidozie Collins Obasi mai shekaru 29 dan Najeriya, bisa zargin damfarar jihar New York sama da dalar Amurka miliyan 30, ta hanyar zamba cikin aminci tare da hadin bakin abokan huldar sa a kasar Canada da sauran sassan duniya.

 Wata sanarwa da ofishin Philadelphia na hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta fitar ta nuna cewa Obasi da tawagarsa sun samu sama da dala miliyan 31 ta hanyar zamba.

Yawancin kudaden da aka ambata sun fito ne daga jihar New York don siyan na'urorin hura iskar oxygen.

FBI ta bayyana cewa Obasi da abokansa sun fara shirinsu na yaudara ne a watan Satumba na 2018 ta hanyar amfani da wani kamfanin bogi dake bawa alumar da sukayi rajista damar yin "aiki daga gida" ta wayar hanunsu. inda suka yi nasarar damfarar su akalla dala miliyan daya.

 Da sake bayyana yadda aka aikata zambar, hukumar FBI ta bayyana cewa Obasi da abokansa sun koma ga sabon salon zamba a lokacin anobar COVID-19 a cikin watan Maris 2020 bayan da Amurka ta kamu da cutar.

Inda suka bayyana a matsayin wakilan wani kamfani na Indonesiya da ke hulɗa da injinan iska da ake tsananin bukata a wancan lokaci, inda suka yi sojan gona cewar su wakilan kamfanin ne da hedkwatarsa ta ​​ke birnin Telford.

Hukumar ta FBI ta bayyana cewa, ta hanyar wannan sabon tsarin, sun samu damar sace dala miliyan 30 daga jihar New York da wasu asibitoci.

 “Wanda ake tuhumar sunyi amfani da wani dillalin naurorin asibiti a Amurka wajen kulla yarjejeniyar cinikayyar wadannan na’urori masu dauke da iskar Oxygen tsakanin su da gwamnatin birnin Newyork kuma a karshe ya yaudari jihar New York bayan da aka tura mishi kudi kimanin dala miliyan 30 don siyan na’urorin da babu su" inji hukumar ta FBI.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci