OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar NDLEA Ta Kama Kwayoyin Miliyan 2.3 Da Akayi Yunkurin Kaiwa Jihohin Arewa

Hukumar NDLEA Ta Kama Kwayoyin Miliyan 2.3 Da Akayi Yunkurin

Hukumar NDLEA tayi nasarar kama kwayoyin kimanin miliyan 2 da dubu dari uku da akai yunkurin shigo da su jihohin arewa 7 domin siyar da su.

Jihohin sun hada da; Borno, Kano, Kaduna, Sokoto, Zamfara, Gombe da jihar nasarawa.

Kakakin hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a yau lahadi a birnin tarayya Abuja. Yace sunyi nasarar kama kwayoyin ne a jerin gwanon sumamen da suka kai a yan kwanakin nan.

Yace kwayoyin da suka kama sun hada da Tramadol, Pregabalin,Hypnox, Diazepam, Exol-5 dakuma akalla kwalabe 7,353 na Akuskura.

Wasu daga cikin masu safarar kwayoyin da akai nasarar kama wa sunhada da; Umar sanusi daga jihar Kaduna, Faruku bello daga jihar sokoto, Osita Nwobodo daga Abuja hadi da wani jika da kaka dake safarar kwayoyi tsakanin Amurka, Dubai da Najeriya a aka kama a filin jirgin murtala Muhammad dake legas.

Shugaban hukumar Birgedier janar Mohammed Buba Marwa mai ritaya. Ya yabawa ma’aikatan bisa namijin kokarin da suka yi. Inda yace su kara kaimi wajen tabbatar da an dakile ta’addar ta’ammali da kwayoyi a fadin kasar nan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci