Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun kama wasu ma’aikatan banki 12 bisa zargin zamba a jihar Enugu.
A cikin wata sanarwa da ta fito a ranar Asabar, ta hannun mai magana da yawun Hukumar Wilson Uwujarem, ya ce jami’anta shiyyar Enugu sun kama wadanda ake zargin ne a ranar Juma’a.
Ta ce binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun sace wasu kudade a wasu asusu da aka dade ba a yi amfani da su ba a reshen wani tsohon banki a jihar.
Hukumar ta bayyana sunayen wadanda ake zargin, Anthony Odeniyi, Onyekachi Deki, Oguchukwu Ene, Chizaram Elendu, Uchenna Anyakora, Kingsley Onah da Elizabeth Akwe.
Sauran sun hada da, Victoria Ezedie, Obinna Chidi-Ukah, Uzochukwu Etoh, Harrison Udeze da Chinenye Acibe.
Hukumar ta EFCC ta kara da cewa "Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike."
0 Tsokaci