OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Halartar Coci Na Ba Shi Da Alaka Da Siyasa – Peter Obi

Halartar Coci Na Ba Shi Da Alaka Da Siyasa – Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya mayar da martani ga mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Ifeanyi Okowa, wanda ya zarge shi da siyasa a ziyarar Coci.

Obi ya ce ba ya dana sani ba kuma wani uzuri da zai bayar na halartar  cocin.

Mai ba wa Obi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Valentine Obienyem ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar, Obi yana halartar duk wani coci da aka gayyace shi.

Obienyem ya ce da gangan masu yin hakan suna alaƙanta ayyukan masu kishin kasa da siyasa.

“Me ya sa dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP zai ce ba daidai ba ne wani ya kai ziyara coci?”

Ya lura da cewa mafi yawan ‘yan Nijeriya rashin shugabanci nagari ne yake damunsu a kasar, don haka ya kamata ayi kokarin dan ganin an dora shugabanci na gari.

Ya ce kamata ya yi a gaya wa gwamnan jihar Delta bambancin dake tsakanin sanin siyasa da kuma shiga harkokin siyasa.

Ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa Obi ba zai gaji da wayar wa ‘yan Nijeriya kaiba game da shugabanci na gari da kuma bukatar ‘yan Nijeriya su kwato kasarsu ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci