OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Dalilin da ya sa muka ayyana yajin aikin sai Baba-ta- gani - ASUU

Dalilin da ya sa muka ayyana yajin aikin sai Baba-ta- gani -

Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, ta bayyana rashin gamsuwarta da Gwamnatin Tarayya kan bukatunta, don haka ta yanke shawarar ayyana yajin aikin sai Baba-ta-gani.

Farfesa Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar ASUU shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a karshen taron gaggawa da kungiyar ta yi a ranar Talata a garin Abuja.

Sanarwar mai taken “Yajin aikin ASUU ceto ne ga jami’o’in gwamnati”.

Idan ba a manta ba malaman jami'o'i sun shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu, bisa gazawar gwamnati wajen cika yarjejeniyoyin da aka kulla da kungiyar.

Wasu daga cikin Bukatun da suka janyo yajin aikin sun hada da batutuwan da suka shafi kudade na jami'o'i, albashi da alawus alawus na malamai da dai sauran su.

Mista Osodeke ya ce an kira taron ne domin duba sake duba abubuwan da ke faruwa tun bayan zaman su na karshe wanda ya sa suka sake tsunduma yajin aikin na tsawon makonni hudu daga ranar 1 ga watan Agusta.

“Saboda abubuwan da aka yi a baya, da kuma tattaunawa mai zurfi kan martanin da gwamnati ta yi a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022, ya zuwa yanzu, kungiyar ta ce ba a biya mata bukatunta yadda ya dace ba “Saboda haka, NEC ta kuduri aniyar sauya yajin aikin zuwa yajin aikin sai baba-ta gani, wanda ya fara daga karfe 12.01 na safe a ranar Litinin, 29 ga watan Agusta 2022, '' in ji shi.

A cewarsa, NEC ta lura cewa kungiyar ta fuskanci yaudara da yawa a cikin shekaru biyar da rabi a tattaunawar da akayi da kungiyar ta ASUU wanda rashin gaskiya yafi yawa a ciki.

Mista Osodeke ya ce ASUU da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa sun nuna rashin jin dadi da kuma alhini kan halin da gwamnatin da Ministan Ilimi, Adamu Adamu suka nuna.

Ya ce don kauce wa shakku,babu daya daga cikin lamarin da ya tilasta wa kungiyar komawa yajin aikin kamar yadda aka lissafa a cikin yarjejeniyar aiki ta FGN-ASUU, MOA, gwamnati ba ta yi magana mai gamsarwa ba har yau.  

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci