OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Da Dumi-Dumi: 'Yan Ta'adda Sun Tare Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

Da Dumi-Dumi: 'Yan Ta'adda Sun Tare Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

Kwanaki hudu da 'yan ta'adda suka kai hari kan jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, wasu 'yan ta'adda da dama sun sake tare hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Sanata Shehu Sani ne ya bayyana hakan a shafin sa na Twitter a ranar Alhamis da yamma.

Idan dai za a iya tunawa, harin da aka kai kan jirgin kasan da ke kan hanyar Kaduna ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da kuma sace wasu da dama.

Shehu Sani ya bayyana cewa, “Yanzun nan ne na samu kira mai daga hankali cewa ‘yan bindiga da dama sun sake tare hanyar Kaduna zuwa Abuja da yammacin yau. Matafiya suna komawa baya cikin gaggawa.”

 

Cikakkun bayanai zasu biyo baya…

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci