OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Da Dumi-Dumi: Umahi Ya Amince Da Kara Wa Ma’aikata Girma Da Biyan 'Yan Fansho

Da Dumi-Dumi: Umahi Ya Amince Da Kara Wa Ma’aikata Girma D

Ebonyi State governor, David Umahi| Photo Source: PremiumTimes

Gwamnan jihar Ebonyi, David Nweze Umahi ya amince da karin girma ga ma’aikatan gwamnati na shekarar 2019, 2020 da kuma 2021.

Amincewar za ta yi tasiri ne kawai ga ma’aikatan gwamnati da suka cancanta a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar Ebony, Hon. Barr Orji Uchenna Orji ya fitar a ranar Litinin.

Gwamnan ya kuma amince da biyan duk ‘yan fansho a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa biyan kudin zai fara aiki ne daga ranar Talata, 22 ga Maris na 2022.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci