OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Bamu da burin karban muhimman kadarorin Najeriya a matsayin biyan bashi - Cewar kasar China

Bamu da burin karban muhimman kadarorin Najeriya a matsayin

Cui Jianchun, Jakadan kasar China a Najeriya, ya ce kasarsa ba ta da niyyar karbe muhimman kadarorin Najeriya a matsayin lamuni idan ta gaza biyan bashin da ta ciwo a kasar.

Jianchun ya bayyana hakan ne yayin da wakilin kasar China Liu Yuxi ya kai wa karamin ministan harkokin wajen Najeriya Zubairu Dada ziyara a ranar Alhamis a Abuja.

Ziyarar wakilin kasar China ta na da nasaba da karfafa dangantakar da ke tsakanin Najeriya da kasar China.

Ya bayyana yadda kasar ta China ta shirya yin aiki da Najeriya domin cin moriyar kasashen biyu.

Jianchun ya ce, China da Najeriya suna aiki ne bisa amincewa da juna, kuma kasarsa ba ta da niyyar kwace kadarorin Najeriya a lokacin da ta gaza biyan bashin da ta karba

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci