OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Atiku Abubakar Ya Musanta Cewa Zai Mika Jami'o'i Gwamnatocin Jihohi Idan An Zaɓe Shi

2023: Atiku Abubakar Ya Musanta Cewa Zai Mika Jami'o'i  Gwam

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce 'yan jarida sun yi masa mummunar fahimta kan maganar da yayi akan jam'i'oi Najeriya.

Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da kafafen yada labarai suka yada cewa zai mika jami’o’in gwamnatin tarayya ga gwamnatocin jihohi idan har aka zabe shi shugaban kasa a 2023.

Mai baiwa dan takarar shawara kan harkokin yada labarai Paul Ibe a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Litinin a Abuja, ya bayyana rahoton a matsayin rahoton kanzon kurege.

Mista Ibe ya ce sun lura cewa anyi wa maganar da Atiku ya fada mummunan fassara,wanda ake ikirarin ya fada ne a zauren taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) karo na 62 dangane da ilimi da kuma yadda za a magance matsalolin da ake fuskanta a fannin.

“Rahoton karya ne, ba gaskiya ba ne, an juya maganar da Atiku Abubakar ya fada yayin da yake amsa tambaya kan batun raba madafun iko, wani muhimmin bangare na tsarin siyasarsa.

“Abin da dan takarar shugaban kasar ya yi magana a kai shi ne shirinsa na raba madafun iko ga sassan tarayya.

"Rahotanni da ya yadu a wasu kafafen yada labarai,ya kasance labari ne na yaudara da karya ga me da abin da ya faru a lokacin da dan takarar shugaban kasa na PDP ya amsa tambayoyi a wurin bude taron NBA," in ji Mista Ibe.

Da yake amsa tambayar da aka yi masa, Atiku ya tuna tattaunawar da ya yi da wani malamin jami’a.

“Atiku Abubakar ya bayar da hujjar cewa makarantu a Amurka a da suna kamanceceniya da jami’o’in farko a Najeriya wadanda suka kasance na gwamnatocin yankin ne.

Ya kara da cewa, idan aka tsara yadda ya kamata da kuma karkatar da madafun iko, jami’o’in gwamnatin tarayya da a yanzu ba su da karfi za a iya sanya su, su tsaya da kyau a karkashin sassan tarayya.

"Ya kara da cewa ilimi zai ci gaba da kasancewa gaba-gaba cikin jerin kudurin gwamnatin sa idan aka zabe shi," in ji Mista Ibe.

Ya bayyana cewa wannan rahoton yaudara ce da aka yi amfani da ita don ganin an shafa wa dan takarar shugaban kasar bakin fenti.

Ya ce rahoton ya kuma haifar da tunanin cewa zai yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyansa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa a watan Fabrairun 2023.

“Muna so mu maido da alkawurran da Atiku Abubakar ya yi na samar da ilimi a matsayin abin da zai kawo sauyi ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki da kuma tsaron kasa." 

“Ya damu matuka game da yajin aikin da malaman jami’o’in suka dade suna yi.

Ya sake jaddada cewa zai sa ido sosai ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) inda Gwamnatin tarayya za ta fi gudanar da ayyukanta yadda ya kamata domin biyan bukatun dalibai da ma’aikatan ilimi,” in ji Mista Ibe.

Mai taimaka wa kan harkokin yada labarai ya bayyana cewa, domin jaddada kudirin Atiku na magance nakasu a tsarin Najeriya, Atiku ya kuma bayyana cewa ya hada kwamitin kwararru a fannin shari’a don rubuta takardar tsarin mulkin shugaban kasa.

Takardar, a cewar Mista Ibe, za ta jagoranci gwamnatin Atiku, idan aka zabe shi, daga ranar farko kan sharudda mulki da albarkatun ga sauran saahin gwamnti.

Ya ce an yi hakan ne da nufin ganin gwamnatin tarayya ta samu kwarin guiwa da kuma yin tasiri a muhimman ayyukanta.

"Muna kira ga kungiyoyin yada labarai da su yi taka-tsan-tsan da labaran da ba su da tushe a matsayin su na wadanda kundin tsarin mulkin kasar ya ba su damar sanar da jama'a da ilmantar da su," in ji sanarwar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci