OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

APC Ta Soke Taron Kwamitin Zartarwa Na Gaggawa

APC Ta Soke Taron Kwamitin Zartarwa Na Gaggawa

Kwamitin Zartarwa na jam'iyyar APC mai mulki ta kasa, ya dakatar da taron gaggawa da ta shirya gudanarwa a yau 17 ga watan Maris na 2022.

Dakatarwar ta biyo bayan umarnin da shugaban kwamitin gudanarwa na jam’iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayar.

An bayyana hakan ne a ranar Laraba a wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren Kwamitin tsare-tsaren jam’iyyar APC, Sanata John James Akpanudoedehe.

Buni wanda tun farko ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan kan rikicin jam’iyyar APC a ranar Laraba ya ce an soke taron da aka ce an shirya yi.

Wani bangare na sanarwar ya bayyana cewa, “Kamar yadda shugaban jam’iyyar kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni yace, an soke taron gaggawa na Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na kasa (NEC) wanda aka shirya yi ranar Alhamis, 17 ga watan Maris na 2022.

A halin da ake ciki, gwamnan jihar Neja kuma mamba a kwamitin riko na jam’iyyar APC, Abubakar Sani Bello, ya mamaye sakatariyar jam’iyyar ta hanyar da ba ta dace ba, yana ikirarin shugabantar jam’iyyar a makon da ta gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa Bello ne ya kira taron na Jam'iyyar da aka shirya gudanarwa a yau wanda Buni ya soke.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci