OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Zaɓen Anambra: Amurka Ta Yi Barazanar Hana Masu Laifin Zabe Biza

Zaɓen Anambra: Amurka Ta Yi Barazanar Hana Masu Laifin Zabe

Hoto Daga: lindaikejisblog

Amurka ta yi barazanar sanya takunkumi da hana biza ga masu katsalandan ga tsarin dimokuradiyya gabanin zaben gwamnan Jihar Anambra.

Ta kara da cewa idanuwan ta na kan duk mai kokarin tada zaune tsaye.

Hakan yazo ne cikin wata sanarwa da sashin hulda da jama’a na ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ta fitar a ranar Laraba.

A cewar sanarwar, hukuncin zai shafi iyalai da 'yan uwan ​​masu laifin zaɓe da masu su iya tada rikici a rumfunan zabe.

A cewar sanarwar, “Za mu mai da hankali sosai kan ayyukan mutanen da ke yin katsalandan ga tsarin dimokuradiyya ko tada tarzoma a kan fararen hula kafin lokacin, ko kuma bayan zaben.

"Ba za mu yi shakka ba wurin hukunci; ciki har da takunkumin biza ga wadanda aka samu da alhakin tashe-tashen hankula masu nasaba da zabe ko kuma lalata tsarin dimokuradiyya."

Gwamnatin Amurkan ta ce tana sa ran a gudanar da zaɓen akan gaskiya da adalci kuma a samu sakamokon da zai yi nuni cewar hakan ra'ayin mutanen Anambra ne.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci