OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zaben 2023: Kwankwaso ya nada jami'an yakin neman zaben sa

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ya nada Dr. Abdulmumin Jibrin Kofa da Barrister Ladipo Johnson a matsayin jami’an yada labaran yakin neman zabensa a shekarar 2023.

A cikinwata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimaki na musamman ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Ibrahim Adam ya fitar, yace kwankwaso ya bukacesu dasu yaɗa angizon jam’iyyar NNPP a dukkanin sassan Najeriya.

Dr. Abdulmumin Jibril Kofa wanda yake da kwarewa a fannin siyasa tsohon dan majalisar tarayya ne daga jihar Kano, kuma yanada kwarewar yin hulda da jama’a musamman a sha’anin siyasa.

Shi kuwa Barrister Ladipo Johnson lauya ne kuma shugaban cibiyar cigaban Kasuwanci da Gudanarwa ta Afirka.

A iya cewa Kwankwaso yabi sahun sauran Yan takarar shugabncin kasa a jam'iyyar APC da PDP wajen nada lauya a matsayin dan yakin neman zaben shi.

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci