OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Za'a zabi kasar da zata zama mai masaukin baki a gasar kallon kafar mata 2027 ta hanyar kuri'a

Za'a zabi kasar da zata zama mai masaukin baki a gasar kallo

Za'a zabi masu masauki baki a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA 2027 ta hanyar kuri'a don yanke tantancewa tsakanin Brazil, da tayin hadin gwiwwar da Belgium, Netherlands, Jamus BNG suka gabatar.

 

 Kunshin neman damar zama mai masauki bakin da kasahen suka gabatar sun cika dukkan sharudda duk da cewa tayin na Brazil ya dara sauran ta fannonin da suka hada da filayen wasanni, masauki masu kyau, wuraren ajjiye abunhawa da hanyoyin sufuri.

 

 Idan har Brazil ta yi nasara, zai kasance karo na farko da za a gudanar da gasar a Kudancin Amurka.

 

 Dukkanin kungiyoyin mambobi 211 na FIFA za su zabi mai masaukin baki a babban taron FiFA karo na 74 da za a yi a Bangkok ranar 17 ga watan Mayu.

 

 Wani rahoto da hukumar kwallon kafa ta duniya ta fitar ya nuna cewa Brazil ta samu maki 4.0 cikin biyar yayin da tayin BNG ya ci 3.7. 

 

Rahoton ya ce: "Abin da ya kamata a lura shi ne, idan har aka yi nasara, Amurka ta Kudu za ta karbi bakuncin gasar a karon farko, wanda zai iya yin tasiri sosai ga wasan kwallon kafa na mata a yankin." 

 

 A makon da ya gabata, Amurka da Mexico sun janye shirinsu na neman karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata a shekarar 2027, inda suka ce za su mai da hankali kan neman damar zama mai masauki bakin a gasar shekarar 2031.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci