OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

'Yan Sanda Sun Kubutar Da Mata 3, Sun Kawar Da 'Yan Ta'adda A Katsina

'Yan Sanda Sun Kubutar Da Mata 3, Sun Kawar Da 'Yan Ta'adda

Biyo bayan kiran gaggawa ga rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina, 'yan sanda sun dakile harin da ‘yan ta’adda suka kai a kauyen Garin Zaki da ke karamar hukumar Batsari.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma ceto wasu mata uku a lokacin da kwace makamai daga hannun ‘yan ta’addan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce lamarin da ya faru a ranar 25 ga watan Afrilun 2022 ya kai ga sace matan uku tare da yin satar shanaye.

Ya kuma bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kutsa kauyen ne akan babura suna harbe-harbe.

Ya kara da cewa, daukin gaggawar da ‘yan sandan suka kai tare da ‘yan banga ne yasa aka ceto matan tare da kwato shanaye 15.

A wani labarin kuma, rundunar ‘yan sandan ta kuma dakile wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a wannan ranar a karamar hukumar Kurfi da ke jihar.

Rundunar ‘yan sandan ta yi nasarar kawar da daya daga cikin ‘yan ta’addan tare da raunata wasu da dama da suka tsere bayan mummunar bata-kashi.

An kwato makamai da alburusai daga hannun 'yan ta'addar da suka hada da dabbobin da suka yi awon gaba da su.

Da yake tabbatar wa jama’a cewa ‘yan sanda za su ci gaba da yin aiki tukuru domin ganin an dawo da zaman lafiya, kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Idrisu Dabban Dauda ya yaba da kokarin jami’an sa da ‘yan banga na nasarar da aka samu kawo yanzu.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ciyar da jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen kame ‘yan ta’addan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci