OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Sanda Sun Damke Wata Mata Da Ta Shirya Yin Garkuwa Da Mijinta

'Yan Sanda Sun Damke Wata Mata Da Ta Shirya Yin Garkuwa Da M

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom a ranar Juma’a ta gurfanar da wata mata mai suna Joy Emmanuel bisa zargin shirya garkuwa da mijinta, Emmanuel Ebong.

Kwamishinan ‘yan sanda, Olatoye Durosinmi, ya shaida wa manema labarai cewa, Joy da masu garkuwa da mutane sun karbi kudi naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa domin a sako mijinta.

Mista Durosinmi ya ce rundunar ‘yan sanda a jihar ba za ta nade hannun ta ga masu aikata laifuka ba. 

Da take bayyana wa manema labarai, Joy ta ce matsoli ne suka tilasta mata shirin yin garkuwa da mijin nata.

Ta ce mijin nata ya bar iyalan sa da yunwa kana baya biya mata bukatun aure. 

"Na yi kananan ayyuka don ciyar da iyalin.

"Na shirya sace shi ne saboda ina bukatar kuɗi don in kula da iyalin.

“Abin takaici, ba a ba ni kudin fansa ba bayan an yi nasarar garkuwa da shi,” in ji ta.

Shi ma da yake magana, Mista Ebong ya ce an yi garkuwa da shi ne da misalin karfe 8.30 na dare, a ranar 21 ga watan Yuli jim kadan bayan shigar sa gida.

“Sun fitar da ni daga harabar gidana a cikin wata karamar bas. 

"Sun tsare ni har na tsawon kwanaki hudu suna neman kudin fansa Naira miliyan biyu.

“Sun kai ni Etinan inda suka tsare ni. 

"Na yi sa'a cewa 'yan sanda sun zo aikin ceto.

"Sun karbo min Naira miliyan biyu.

"Daga baya ‘yan sanda sun kwato kusan N500,000 daga hannunsu,” inji shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci