OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Yakamata Jami'o'i Su Fara Gwajin Shaye-shaye Ga Duk Dalibai, Cewar Marwa

Yakamata Jami'o'i Su Fara Gwajin Shaye-shaye Ga Duk Dalibai,

Brig. Gen. Mohamed Buba Marwa (Retd.) | Hoto Daga: Freedom Radio

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya yi kira da a yi gwajin kwaya ga dukkan daliban da ke karatu a Jami'o'i.

Marwa ya ce ya kamata Jami'o'i su dauki gwajin kwaya ga sabbin dalibai da masu dawowa a matsayin wani mataki na dakile shan muggan kwayoyi.

Yayin da yake bayyana bukatar kare rayuwar matasan kasar nan, ya ce hukumar ta NDLEA na fatan hada hannu da dukkan Jami'o'i domin kafa wurin gwaji a harabar su domin kawo karshen matsalar shan muggan kwayoyi.

Marwa ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake kaddamar da shirin yaki da miyagun kwayoyi a jami’ar Abuja ranar Laraba.

A nasa jawabin, ya ce, “Daga cikin matakan da za a dauka na rage shaye-shayen miyagun kwayoyi a jami’ar, shi ne shirin kaddamar da gwajin Shaye-shaye ga sabbin dalibai da masu dawowa. Ana sa ran gwajin shan miyagun ƙwayoyin zai iya zama tsarin yaƙi da miyagun ƙwayoyi ga duk manyan makarantun koyo a Najeriya."

Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu wanda ya samu wakilcin mataimakin darakta, kan bayar da shawarwari a ma’aikatar, Okereke Chinwe, ya ce ma’aikatar na yin kokari wajen ganin ta kara kaimi wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.

Shugaban jami’ar, Farfesa Abdul-Rasheed Na’allah a lokacin da yake yaba wa hukumar ya ce jami’ar za ta ci gaba da jajircewa wajen yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci