OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar NDLEA Ta Gano Kwayoyin Tramadol Miliyan 13 A Lagos

Hukumar NDLEA Ta Gano Kwayoyin Tramadol Miliyan 13 A Lagos

NDLEA Officials

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta gano kwayoyin Tramadol miliyan 13 a wani katafaren gida da ke unguwar Lekki a jihar Legas.

 

 Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

 

 A cewar Babafemi, gidan na wani mai safarar kwayoyi ne wanda aka kama kuma a yanzu haka yana tsare.

 

 Ya kara da cewa an kwato kwayoyin Tramadol miliyan 13 a gidan.

 

 Femi Babafemi ya Kara da cewar Babu Wani mahaluki da yake zaune a katafaren gidan, ana amfani da shi me kawai domin ajiyar Kwayoyi domin batar da hankalin mahukuntan.

 

 Wannan ci gaban ya zo ne kwanaki bayan hukumar NDLEA ta fasa wani dakin ajiyar kaya a yankin Ikorodu da ke jihar inda ake ajiye hodar iblis.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci