OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Yadda 'Yan Gudun Hijira A Borno Suka Haifa Jarirai 17,053

Yadda 'Yan Gudun Hijira A Borno Suka Haifa Jarirai 17,053

Photo source: Wikipedia

Hukumar kula da kaura ta duniya IOM ta ce an haifi jarirai 17,053 a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke fadin jihar Borno a cikin shekaru 3, in ji wata rahotar BBC Hausa.

IOM ta fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa kamar yadda aka yi rajista daga shekarar 2019 zuwa 2021, an haifi jariran ne a sansanoni 18.

Shugaban na IOM, Mista Frantz Celestin ya bayyana cewa kungiyar ita ce babbar mai ba da tallafi a yankin Arewa maso Gabas tare da daukar sansanoni 115 da ke karkashin kulawar ta.

Ya kara da cewa kungiyar ta hada gwiwa da hukumar kidaya ta Najeriya da Kuma Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya don ba da takardun shaidar haihuwa ga jariran.

Ya ce a matsayin daya daga cikin ayyukan kungiyar na tattara bayanai don bayar da taimako ga masu ba da tallafi a shiyyar Arewa maso Gabas, bayar da takardar shaidar haihuwan zai tallafa matuka. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci