OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Zulum Ya Tarbi Mata Shida Da Suka Tsere Daga Hannun Boko Haram

Zulum Ya Tarbi Mata Shida Da Suka Tsere Daga Hannun Boko Har

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum| Hoto Daga: Guardian

 

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya tarbi 'yan mata shida da suka tsere daga hannun Boko Haram.

 

Sama da shekara guda kenan da aka sace su da 'ya'yansu tara.

 

kwamishinar harkokin mata, Hajiya Zuwaira Gambo ce ta gabatar da ‘yan matan da suka tsere masu shekaru tsakanin 20 zuwa 25.

 

A cewar ta, 'yan matan sun tsere daga hannun‘ yan ta’addan a Buni Yadi dake jihar Yobe, sannan suka yi tafiyan awanni 6 ta dajin Sambisa kafin jami’an tsaro su kubutar da su.

 

Ta kara bayyana cewa “An sace uku daga cikinsu a ranar 3 ga watan Oktoba na 2020, yayin da aka sace sauran a ranar 5 ga watan Mayu na 2021. Uku daga cikinsu da aka sace a kauyen Takulashu na Chibok su ne Maryam Ishaya tare da yaro guda; Rachael Simon da yara biyu; Esther Ayuba da yara biyu; Alheri Ezekiel, wanda ke da yara biyu, Victoria Andrew da Victoria James, wadanda su ma suna tare da yara biyu, an sace su daga ƙauyen Cofure, Garin Hong na Jihar Adamawa."

 

Zaku tuna cewa, a ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne 'yan ta'addan Boko Haram suka mamaye makarantar sakandaren' yan mata ta Chibok inda suka sace dalibai mata sama da 200, kuma tun daga lokacin sama da 100 daga cikinsu suka tsere yayin da aka sako wasu bayan tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan ta'addan.

 

Zulum ya karɓi waɗanda suka tseren da yaransu cikin farin ciki a ofishinsa da ke Sakatariyan Musa Usman dake Maiduguri.

 

Wadanda suka halarci taron sun hada da wasu iyaye, shugaban ƙaramar hukumar Chibok, Alhaji Umar Ibrahim, sarakunan gargajiya, masu ruwa da tsaki ciki har da shugaban ƙungiyar Kiristoci na Najeriya (CAN), reshen Borno, Bishop Mohammed Williams Naga.

 

Zulum ya ce gwamnati na yin duk kokarin ta na tabbatar da sake ginawa da kuma dawo da duk wadanda harin ta’addancin Boko Haram ya rutsa da su.

 

A cewar sa, “Na yi matukar farin cikin karbar ku, 'ya'yana, bayan da kuka fada hannun 'yan ta’addan Boko Haram. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya kubutar da ku, Ya kuma kare ku daga hannun ‘yan ta’addan. A matsayinmu na gwamnati, za mu yi duk mai yiwuwa don tallafa muku don ci gaba da rayuwa ta yau da kullun a cikin al'umma yayin da muke mika ku ga dangin ku.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci