OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yadda Wani ango, da wasu mutum shida suka rasa ransu a Enugu

Yadda Wani ango, da wasu mutum shida suka rasa ransu a Enugu

 A ranar Asabar din da ta gabata ne aka tsinci gawarwakin mutane shida ciki har da ango a garin Akutara da ke yankin Adani a karamar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Enugu. 

Wadanda abin ya shafa sun halarci wani daurin aure na gargajiya a ranar Juma’a a garin Obollo-Eke da ke karamar hukumar Udenu a jihar.

Bayan daurin auren suka sake shirya wani shagali.

Sai dai an wayi gari an same su a mace. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce a washegari da safe an lura cewa cikin 'yan shagalin bikdn ba bu wanda ya fito daga daki,sai da aka bude kofar,a sannan ne aka iske su gaba dayansu a mace suna zubar da kumfa a bakinsu.

“Nan take aka kai su asibiti, inda aka tabbatar da mutuwar shida daga cikinsu, an ajiye gawarwakin a dakin ajiye gawa, yayin da sauran da su ka tsira ke karbar magani,” inji shi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmed Ammani, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin, in ji Mista Ndukwe.

Mista Ammani ya jajantawa iyalai da abokan mamatan. Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su samar da zaman lafiya ta re da kuma tallafa wa ‘yan sanda da “bayanan da za su taimaka wajen gudanar da bincike.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci