OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Tsaro Da Tattalin Arziki Ne Manyan Batu Yayin Ganawar Gwamnan Gombe Da Takwarorin Sa

Tsaro Da Tattalin Arziki Ne Manyan Batu Yayin Ganawar Gwamna

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya| Hoto Daga: ThisNigeria

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya gana da takwarorin sa na yankin Arewa Maso Gabas inda suka tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki da tsaro.

 

Gwamnan tare da gwamnan jihar Borno kuma shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso gabas, Babagana Umara Zulum sun gana a taron kungiyar karo na 6 a Damaturu jihar Yobe.

 

Sauran mutanen da suka halarci taron sun hada da mai masaukin baki Gwamna, Mai mala Buni da mataimakan gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi da Taraba.

 

Da yake bayyana bude taron, shugaban kungiyar ya ce kungiyar ta gano kalubale daban-daban da yankin ke fuskanta a tarukan da ta yi a baya.

 

Ya kara da cewa an bayar da shawarwarin magance kalubalen baki daya domin inganta rayuwar jama’a.

 

Zulum ya bayyana manyan kalubalen shiyyar da Najeriya a matsayin na tsaro da tattalin arziki.

 

Ya ce wannan ya hada da "tashe-tashen hankula, 'yan fashi, garkuwa da mutane, satar shanu da kuma cin zarafi tsakanin jinsi da sauransu."

 

Ya kuma kara da cewa abin dubawa ne yadda alkaluman rashin aikin yi da fatara ke karuwa wanda ke da illa ga tattalin arziki.

 

Zulum ya ce kungiyar ta himmatu wajen ganin an cimma nasarar shiyyar ta hanyar azama da zuciyar aiki.

 

Gwamna mai masaukin bakin, Mai Mala Buni ya yaba da jajircewar kungiyar wajen samar da zaman lafiya a yankin.

 

Ana sa ran kungiyar zata fitar da sanarwar a karshen taron.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci