OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Shekarau na shirin ficewa daga jam'iyyar NNPP zuwa PDP yayin da Atiku ya yi masa ta yi masu tsoka

Ana sa ran nan gaba, tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, zai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, zuwa PDP, bayan wasu alkawaruka masu tsoka da ake zargin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi masa.

Shekarau, wanda ke wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP a hukumance a wata wasika da ya aikawa shugaban majalisar, Ahmad Lawan a ranar 29 ga watan Yuni.

Duk da an basa tabbacin samun tikitin takarar Sanata a jam'iyyar NNPP, jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa an sami rahoto Malam Shekarau ya sidade ya dira jihar lagos a ranar 24 ga watan Yuni domin ganawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi a burin sa na zama mataimakinsa.

An tattaro cewa tattaunawa da jam’iyyar Labour ta ruguje ne bayan da shugabannin APC da PDP suka fara kokarin ganin tsohon gwamnan ya dawo bangaren su.

Ko da shugabannin NNPP suka samu labarin ficewar Malam Shekarau, tawagar mutum 3 da suka hada da dan takarar gwamnan jihar NNPP Abba Kabir-Yusuf, da dan takarar kujerar Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila da kuma dan takarar majalisar wakilai Kabiru Rurum, suka nemi ganawa da shi a daren Juma'a a Abuja, wanda hakan ya ci tura.

Majiya mai tushe da ke da masaniya kan yunkurin Malam Shekarau da kuma ganawar sa da dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar; ta re da abokin takararsa Ifeanyi Okowa da; Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyochia Ayu, ya ce tsohon gwamnan ya “yi yarjejeniya” da jam’iyyar PDP kuma ana sa ran nan ba da dadewa ba zai bayyana ficewar sa a hukumance.

A cewar wani mai sharhi, a ranar Lahadin da ta gabata ne tsohon gwamnan ya kira taron gaggawa na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, wadda aka yi wa lakabi da Shura Consultative Assembly, inda ya sanar da ‘yan majalisar halin da ake ciki.

DAILY NIGERIAN  ta tattaro cewa kwamitin mutum 21 zai gana a yau Talata da misalin karfe 4 na yamma don kammala shirye-shiryen sauya sheka da kuma hanyoyin da za a bi wajen tafiyar da sukar jama'a da ka iya biyo bayan tafiyar Malam Shekarau.

Wata majiya ta bayyana cewa a wani bangare na shirin ficewar dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar zai zo gidan Malam Shekarau dake Mundubawa domin yi masa tarba kafin daga baya a fitar da sanarwar.

A halin da ake ciki Atiku ya yi wa Mallam wasu tayi masu tsoka irin su minista da sauran su. Bugu da kari kuma za a nada shi a matsayin kodinetan yakin neman zaben yankin Arewa maso Yamma kuma mai kula da kudaden yakin neman zabe a yankin,” Cewar majiyar.

Sai dai wata majiya ta kusa da Malam Shekarau ta ce Sanatan ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar NNPP ne ya yi watsi da takararsa na Sanata saboda jam’iyyar NNPP ta kasa karbar wasu daga cikin mukarrabansa.

“Jam’iyyar NNPP ta ba Shekarau tikitin takarar Sanata ne ba tare da baiwa abokan sa tikitin takara ba. Don haka akwai tsananin bacin rai a tsakanin abokan Shekarau da suke ganin cewa Mallam kujerarsa ta Sanata kawai ya nema bai nema musu ba,” inji majiyar. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci