OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

NNPP Ba Zata Ruguza Tsarinta Ga Tinubu Ko Atiku Ba, Cewar Shugabanta

NNPP Ba Zata Ruguza Tsarinta Ga Tinubu Ko Atiku Ba, Cewar Sh

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta musanta duk wani yunkuri na ruguza tsarin jam’iyyar dan alaka sauran jam’iyyun siyasa.

Shugaban jam’iyyar na kasa Farfesa Rufa’i Alkali, ya ce jam’iyyar ba ta shirya mika halascinta a matsayinta na jam’iyyar siyasa mai rijista ga wata jam’iyya ba.

Alkali, wanda ya zanta da manema labarai a Legas, yayin mayar da martani kan rade-radin da ake yi na cewa magoya bayan dan takararta na shugaban kasa, kuma jagoran jam’iyyar na kasa, Sanata Rabi’u Kwankwaso, na tattaunawa da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yayin mayar da martani kan batun, shugaban NNPP, ya ce tuni aka rufe tsarin hadaka tsakanin jam’iyyun siyasa.

Yayin da ya ba da misali da ka’idojin zaben shekarar 2023 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar.

Rufa'i ya kuma yi magana game da ficewar tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau daga jam'iyyar a kwanakin baya, inda ya ce jam'iyyar na mutunta matakin da ya dauka amma "ba za mu bari hakan jawo wata rigima ba."

Ya tabbatar da cewa jam’iyyar zata ci gaba da kasancewa zabi fiye da APC da PDP sannan ya ce duk wani kawance da wasu jam’iyyu gabanin zaben zai kasance a kan hadin gwiwa.

 

​​​​​​​​​

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci