OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane miliyan 50 yanzu suna rayuwa cikin bautar zamani a duniya - ILO

Mutane miliyan 50 yanzu suna rayuwa cikin bautar zamani a du

Akalla mutane miliyan 50 ne ke rayuwa a cikin bautar zamani a duniya ciki har da Najeriya, in ji kungiyar kwadago ta duniya ILO.

Wannan na kunshe cikin rahoton Ƙididdiga ta Duniya na Bautar Zamani, na 2021 da ILO ta gabatar. Daga cikin adadin mutane miliyan 28 an tilasta musu yin aikataum, mutum miliyan 22 Kuma anyi musu auren dole.

Adadin mutanen da ke cikin bautar zamani, kamar yadda kungiyar ta duniya ta koka, ya karu sosai a cikin shekaru biyar da suka gabata, tana mai cewa “ karin mutane miliyan 10 ne ke cikin bautar zamani a shekarar 2021 idan aka kwatanta da kiyasin 2016 a duniya Wadanda suka haɗa da Mata da Kananan yara wadanda sun kasance masu rauni sosai a cikin aluma”

 

ILO ta yi bayanin cewa “Bautar zamani tana faruwa a kusan kowace ƙasa a duniya, a tsakanin kowacce ƙabila, al’adu da addini.

A cewar rahoton, “Kimanin mutane miliyan 22 a ke yiwa auren dole a kowace rana a shekarar 2021. Hakan ya nuna an samu karuwar miliyan 6.6 tun bayan kiyasin 2016. Wannan alamarin musamman yafi shafar yara masu shekaru 16 zuwa ƙasa mai yiyuwa ne nesa ba kusa ba fiye da kiyasin yanzu hakan yasa ake ɗaukar auren yara a matsayin tilastawa saboda yaro ba zasu iya ba da izinin auren doka ba.
Kaso 86 cikin dari na aikatau na dole kuwa ana samun su a cikin kamfanoni masu zaman kansu. Gwanativin kasashe sun tilastawa kashi 14 cikin 100 na masu aikin tilas. Kusan ɗaya cikin takwas na duk waɗanda ke aikin tilasta yara ne (miliyan 3.3). Fiye da rabin waɗannan suna cikin cin zarafin tilasta musu suyi karuwanci.

Da yake tsokaci akan lamarin , Darakta-Janar na ILO, Guy Ryder, ya ce "Abin mamaki ne yadda yanayin bautar zamani ba ya raguwa a koda yaushe.Mun san abin da ya kamata a yi, kuma mun san za a iya yi. Hakika Ingantattun manufofi da ka'idoji na kasa suna da tasiri amma gwamnatoci ba za su iya dakile Matsalar su kaɗai ba. Sai an hada hannu da Kungiyoyin kwadago, kungiyoyin ma’aikata, kungiyoyin farar hula da alumma baki daya duk suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen dakile wannan ta'adda" 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci