OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Motar Dakon Mai Ta Kama Da Wuta A Kaduna

Motar Dakon Mai Ta Kama Da Wuta A Kaduna

Wata motar dakon mai ta kama da wuta a safiyar yau, a yankin karamar hukumar Soba dake jihar Kaduna a safiyar yau.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe goma na safiyar Lahadi a lokacin da tankar ta kai mai a gidan man Shirash da ke hanyar Jos.

Babu tabbaci kan yadda wutar ta tashi sai dai shaidu sun ce tana cikin sauke man fetur ta kama da wuta, haka kuma babu wanda ya jikkata ko kuma ya rasa ransa.

Rahotanni sun ce motocin kashe gobara har uku sun kai ɗauki inda suka taimaka wurin kashe wutar.

Haka ma jami'an tsaro sun je wajen da lamarin ya faru domin sa ido.

Ko a watan Janairun da ya gabata, sai da aka yi gobara sau 114 a yankunan Kaduna da Zaria da kuma Kafanchan duk a Jihar Kaduna kamar yadda hukumar kashe gobara ta jihar ta bayyana.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci